Sojojin Najeriya basu da hannu a harin da aka kai wa gwamna Zulum Boko Haram ne

Sojojin Najeriya basu da hannu a harin da aka kai wa gwamna Zulum Boko Haram ne

Hedikwatar tsaron Najeriya ta musanta zargin ke cewa sojoji ne suka kai hari ga ayarin motocin gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zullum.

A cewar sojin, ‘yan Boko Haram ne suka kai hari, ba kamar yadda ake cewa zagon kasa ne daga wajen jami’an tsaro.

A kwanakin kadan da suka wace ne, wasu masu dauke da makamai suka bude wuta kan ayarin gwamnan lokacin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa garin Baga domin wata ziyarar aiki.

An shafe mako daya kafin rundunar sojin kasar suka mayar da martani kan wannan zargin da suka kira mai nauyi a bainar jama’a, duk da yadda gwamnan ya sha fada yana nanata zargin nasa.

Yayin wata hira da gidan talabijin din Channels mai zaman kansa a Najeriya, babban jami’in watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar John Enenche ya bayyana cewa, sakamakon binciken da suka yi kan bidiyon harin, ya nuna cewa mayakan Boko Haram ne suka kai harin, ba sojojin kasar ba kamar yadda gwamma Zulum yayi zargi.

“Don haka mun yi bincike kan bidiyon nan take kuma mun gano cewa sashen tsara dabarun yaki bai da hannu a ciki,”, in ji Manjo Janar Enenche.

Ya kara da cewa “Mun yi wa bidiyon nazari na tsanaki. Ko daga karar harbe-harben, za ka fahimci cewar ba karar irin makaman da muke amfani da su bane. Idan ka jima kana fada da abokin gaba to za ka kai matakin da duk wasu halayensa za ka fahimcesu”.

Janar Enenche ya kara da cewa masu ruwa da tsaki a lamarin za su dauki mataki kan wannan batun.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More