Ta tabbata Buhari ya kori shugaban hukumar inshorar lafiya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da korar babban sakataren hukumar Inshorar lafiya ta kasar wanda ya sha fama da dambarwa.

An tura Farfesa Usman Yusuf hutun dole ne a watan Oktoban daga gabata  bayan majalisar gudanarwar hukumar ta dakatar da shi.

Daraktar yada labarai a ma’aikatar lafiyar Najeriya, Boade Akinola ta cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ta ce korarsa ta zo ne bayan shawarar da kwamitin binciken da aka kafa don gano sanadin rikicin da ya dabaibaye hukumar, ya bayar.

Tun farko a shekara ta 2017 ne tsohon Ministan Lafiyan kasar, Farfesa Isaac Adewole ya dakatar da Farfesa Yusuf bisa zargin aikata ba daidai ba, da kuma tafka almundahana da dukiyar al’umma.

Sai dai kwararren likitan ya sha musanta zargen, inda yake cewa yan adawa ne suke yakarsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More