Taron Ecowas a Nijar: Abunda shugaba Buhari ya fada

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi shugabannin kungiyar ta  cigaban tattalin arzikin kasashen Afirika ta Yamma ECOWAS kan tsawaita mulkinsu yana mai cewa hakan babban hatsari ne.

Ya bayyana haka ne a Jamhuriyyar Nijar a ranar Litinin, inda shugabannin suka hadu don tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi yankin.

Taron na kwana daya, kuma shi ne irin sa na 57,  an gudanar da shi ne a Yamai, babban birnin ƙasar.

Taron ya tattauna kan yanayin da ake ciki a Mali bayan juyin mulkin da soji suka yi wa Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ranar 18 ga Agusta lamarin da ya sa ECOWAS ta sanya wa kasar takunkumi.

Shugabannin kasashen Najeriya da Senegal da Cote d’Ivoire da kuma Burkina Faso na daga cikin mahalarta taron.

Shugaba Buhari ya bukaci takwarorinsa na ECOWAS su daina tsawaita mulkinsu domin hakan “yana zama silar matsala”.
“A matsayinmu na shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS, akwai bukatar mu yi biyayya ga kundin tsarin mulki kasashenmu, musamman game da wa’adin mulki. Wannan fanni ne da ke haifar da rikici da dumamar yanayin siyasa a kasashenmu,”inji Buhari kamar yadda sanarwar da mai magana da yawun  Shugaba Buhari ya fitar a yammacin ranar ta Litinin din.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More