Tattaunawar Adamu Zango da Jafar Jafar M46 na kudin makarantar yaran da ya biya

Tun safiyar yau misalin 10:03 na tuntubi Adam A. Zango don na ji daga bakinsa, sai ya ce min yana kan haryarsa ta zuwa Kaduna daga Sokoto. Ban sake nemansa ba sai a daren nan.
Na jima ina aikin bin diddigi a harkar jarida kuma yau-da-gobe ta sa za ka iya gano bakin zaren in ka nemi magana daga tushe. Wasu za su iya tunanin ko hassada ake yiwa Adam Zango akan an bi ba’asin maganar. A fahimtata ta aiki fayyace gaskiya da bin diddigi nauyi ne da ya rataya akan mai aikin jarida.

Kafin na tuntubi Zango, na tuntubi makusantansa da abokansa don jin tabbacin batun biyan miliyan 47 da ya yi ikirarin biyan wata makarantar abokinsa wato “Prof. Ango Abdullahi School” don biyawa marayu 101 kudin karatu. Duk bayanansu babu mutum daya da ya ce min gaske ne. Na tattauna da Ibrahim Sheme, wanda shi ne mawallafin Mujallar Fim, wanda kuma ya san ciki da wajen Kannywood ya ce min ya yi bincike sosai ya gano cewa babu sahihanci a batun biyan kudi.

Da misalin karfe 9:46 na daren yau na sake rangadawa Adam Zango waya don jin tabakinsa. Na tambayi Adam Zango shin ko zai iya nuna min shaidar takardar banki da ya biya kudin ko kuwa a hannu ya dankawa makarantar kudin?
Adam Zango ya kekashe kasa ya ce ai shi ba don riya ya yi ba, shi don Allah ya yi, saboda haka ba zai bada takardun a gani ba.
Ya kara dai cewa: “Duk wadanda ba su yarda ba su je makarantar su tabbatar.” A zuciyata na ce ai principal dan amshin Shata ne, sai yanda aka kitsa masa zai fada. Hasali ma ni har yanzu banga takardar banki da aka buga hatimi aka rattabawa hannu ba.

Sai na ce masa to ai Shamsu (mai makarantar) abokinka ne, don kuwa tare da shi ma ku ka je Zamfara yau. Wasu suna ganin kamar gidoga ku ka shirya.

Sai Adam Zango ya ce: “Shamsu maigida na ne ba abokina ba. Kuma na ga me ka rubuta a Facebook; Tunda ba ka yarda ba, ban ce dole sai ka yarda ba.” Na sake tambaya shin ko zai iya rantsuwa da Alkur’ani mai girma kamar yadda ya yi a ‘yan kwanakinnan cewa ya biya miliyan 47 a asusun makarantar?
Sai ya ce: “Akan me zan rantsi bayan nace bazan sake rantsuwa ba”
Cc:Northflixing

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More