Tauraron fina-finan India Amitabh Bachchan ya warke daga Covid-19

An sallami fitaccen tauraron fina-finan India, Amitabh Bachchan, daga asibiti bayan ya warke daga cutar Covid-19.

A watan da ya gabata ne Mista Bachchan mai shekara 77 ya fitar da sanarwar ya kamu da cutar Covid19 a shafinsa na Twitter.

A ranar Lahadi 2 ga watan Agusta ne ya bayyana cewar, ya bar asibiti bayan ya warke daga cutar.

Inda yayi godiya wa magoya bayansa bisa addu’o’in da suka yi masa, da kuma ma’aikatan asibitin Nanavati da ke Mumbai bisa “kwarewarsu” ta aiki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More