Tawagar Gwamnatin Najeriya sun Isa Senegal wajen ta’aziyyar Sheik Khalifa Ahmed Tijjani Inyass

Tawagar Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari ta isa Senegal domin ta’aziyyar rasuwar jagoran Dariƙar Tijjaniya a Afrika wato Sheik Khalifa Ahmed Tijjani Inyass.

Wayanda suka je kasar yin ta’aziyyar amadadin Shugaba Muhammadu Buhari, akwai Shugaban hukumar kula da shige da fice ta Najeriya Muhammed Babandede.

Marigayi Sheik Khalifa Ahmed Tijjani Inyass ya rasu, a wannan makon ne, kuma tuni aka yi jana’izarsa a birnin Kaulaha da ke kasar ta Senegal.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More