
Thiago Alcantara ya harbu da COVID-19
Thiago Alcantara ya harbu da COVID-19
Liverpool za ta kasance ba tare da Thiago Alcantara nan gaba ba
bayan dan wasan tsakiya na Sifen ya harbu da cutar mashako COVID-19, Thiago Alcantara zai killace kanshi har sai sanda aka tabbatar ya warke daga cutar inda bazai samu damar buga wasan da kungiyar sa za ta buga da Arsenal a ranar Litinin a Anfield.
Thiago ba zai taka leda ba na makwanni biyu masu zuwa.
Wasan da zai tsallake sun hada da Arsenal a gasar cin kofin Carabao
da Aston Villa a gasar Premier.