Tilas INEC ta rika yiwa yan kasa bayanin kan gudanar da zabe

Kwamitin Kamfen na dan takaran Shugabancin kasar Najeriya  karkashin  na Jam’iyyar APC, ta ce kamata tilas hukumar zabe mai zaman kanta, wato INEC ta kasa ta rika yi wa al’umman kasar ta Najeriya  bayanin irin shirin da take yi na gudanar da babban zaben kasar a ko wanda lokaci.

Kwamitin kamfen din ya yi wannan bayanin ne a bisa yanda hukumar zaben ta dage zaben.

Da yake magana da manema labarai, shugaban sashen shirya zabe da lura da harkokin zaben, Babatunde Fashola, da Hadiza Bala-Usman, shugabar sashen tuntuba da samar da kayan aiki, sun nuna rashin jin dadin su a kan shawarar da INEC din ta yanke na dage zaben.

Fashola ya ce, Jam’iyyar APC ba za ta karbi uzurin hukumar ta INEC ba a kan yanda ta hana ‘yan Najeriya sauke hakkin su.

A kan wannan, milyoyin ‘yan Najeriya sun sadaukar da lokutan su, dukiyarsu da dawainiyarsu domin su sauke hakkin da ke kansu, sai kwatsam dage zaben.

Matsayin shirin da INEC ta yi na samar da kayan aikin zaben, musamman ma, ‘yan Nijeriya za su so sanin ko duk kayan zaben da ake bukata suna cikin kasan nan a halin yanzun, in kuma ba su a cikin kasan nan, wane shiri hukumar ta yi na tabbatar da an shigo da su.

Za su so sanin shirin da hukumar zaben ta yi na aikewa da kayan zaben kafin ranar ta 23 ga watan Fabrairu.

 

Kan  daukar  matakai na samar da kayan jigilan kayan zaben zuwa duk sassan kasar nan, kamar maganan, motoci, Jiragen ruwa, manyan motoci, Jiragen sama, Jiragen Helikwaftoci, leburori da kuma kudaden da hukumar ta INEC duk za ta yi amfani da su wajen gudanar da zabukan na 23 ga watan Fabrairu da na 9 ga watan Maris. “Bugu da kari, za mu so INEC a kullum ta rika yi wa al’umma bayanin halin da ake ciki har komai ya kammala.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More