Tinubu ya bukaci gwamnatin tarrayya ta yi amfani da BVN wajen bada tallafi

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Najeriya, Sanata Bola Tinubu, ya bukaci gwamnatin tarayya ta yi amfani da lambar tantance asusun banki wato BVN  wajen aika wa ‘yan Najeriya kudin tallafin, a yunkurin tana rage radadin matsin da annobar covid-19 ta haifar, wanda ake fama dashi a kasashen Duniya baki.

Tsohon gwamnan jahar Legas din ya bayar da shawara hakan ne  cikin wani jawabi da ya fitar a Legas, a jiya Laraba 15 ga watan Aprilu 2020.

Inda Ya ce za a iya biyan kudi kai tsaye zuwa asusun wadanda za su ci moriyar tallafin ta hanyar amfani da BVN dinsu.
Inda  ya kara da cewa, za a fi samun tsaro ta hanyar tura kudi zuwa asusu kuma hakan zai kawo karshen rigingimun da ake samu a lokacin rabon kudin hannu da hannu.

Sannan  hakan zai kara jawo dumbin jama’a, musamman talakawa mazauna kauyuka, su bude asusun banki. “Akwai gidajen talakawa da ke bukatar abinci, ruwa, da sauran abubuwan more rayuwa.
Akwai bukatar nuna tausayi ga irin wadannan mutane.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More