Tinubu ya kalubalanci Saraki da Dogara kan kasafin kudi Najeriya

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu ya zargi shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da yin aringizo a kasafin kudi na tsawon shekaru hudu da suka yi suna jagorantar majalisun tarayya.

Tinubun ya zargi, shugabannin majalisar biyu da aringizon ta hanyar sanya wasu ayyukan da naso ne na kashin kansu a cikin kasafin kudin, sannan suna zabge kasafin da an sanya shi ne cikin kasafin kudin don amfanin al’ummar Najeriya.

Tinubu ya yi wannan zargin ne a wata sanarwa da ya saki ranar Lahadi, ta hanyar hadimin shi na sashen watsa labarai, mai suna Tunde Rahman.

A lokacin da Tinubun ya ke mayar da martani kan goyon bayan da ake zargin yana bai wa wasu mutane, a turka-turka shugabancin majalisun tarayya da ake yi, inda ake zargin Tinubu yaba goya musu baya ne don ya na sha’awar zama shugaban kasa Najeriya a Shekarar 2023.

Amma tsohon gwamnan jahar Legas din ya bayyana cewa ba manufa ta siyasa ba ce a gabanshi, abinda ya fi damun shi shi ne kada a maimaita shugabancin majalisun irin salon Saraki da Dogara, don haka yake bai wa Shugaban kasa Buhari goyon baya wajen ganin an zabo shugabannin majalisar da suka dace da muradun jam’iyyar APC.

Yanzu irin yadda Saraki da Dogara da ‘yan barandansu, suka yi katutu a majalisun tarayya, sannan suka dinga kawo cikas, tsaiko da aringizo a kasafin kudin, kusan shekaru hudu suna ta yin hakan, don haka dole mu taka ma ire-irensu birki. ’ inji Tinubu

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More