Tsarin rufe iyakokin Najeriya: Kwalliya na biyan kudin sabulu – Buhari

Shugaban kasar Najeriya  Muhammadu Buhari, ya ce kwalliya na biyan kudin sabulu dangane da matakin gwamnatinsa na wucin gadi kan rufe kan iyakokin kasar.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne yayin ganawa da wata tawagar kungiyar yan kasuwa, masana’antu, da kuma manoma a Abuja, inda ya ce a halin da ake ciki tattalin arzikin Najeriya ya soma amfana da matakin rufe iyakokin, wajen  yakar matsalar shigar da kayayyaki cikin kasar ta hanyar fasakauri.

Kwanaki da suka wuce kadan  kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Africa ECOWAS, ta shawarci gwamnatin Najeriya ta janye matakin na rufe kan iyakokinta, saboda illar da matakin zai yiwa shirin yankin na yammacin nahiyar ta Afrika, na gudanar da tsarin hada-hadar kasuwancin bai daya.

Inda shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa na nan kan bakanta na goyon bayan tsarin kasuwancin bai daya tsakanin kasashen kungiyar ECOWAS, da kuma nahiyar Afrika baki daya, yarjejeniyar da ya sanyawa hannu a watannin baya.

Sai dai shugaban ya ce tilas a gudanar da tsarin kasuwancin na bai daya, bisa yadda  tsarin doka ta tanadar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More