
Tsohon gwamna Yari ya kalunbalanci wata kafar watsa labarai kan zargin rahoton karya
96
Normal
0
false
false
false
EN-US
X-NONE
X-NONE
/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}
Tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdulaziz Abubakar Yari, ya yi barazanar daukar mataki da hukunce-hukunce na shari’a a kan wasu kafofin watsa labarai 3 da ke yada rahotanni kamar yadda ya bayyana a matsayin karairayi a kansa.
Lamari ya biyo bayan simamen na bazata da hukumar hana yiwa tattalin arziki ta’annati EFCC ta kai gidansa dake garin Talata Mafara a ranar 4 ga watan Agusta 2019.
Wanda ya janyu daya daga cikin kafofin watsa labaran ta yi soki burutsu na bayyana wani rahoto da ke nuni da cewa, jami’an hukumar EFCC sun yi kacibus da motoci 21 na alfarma a gidan tsohon gwamnan yayin gudanar da bincikensu inji Dorasa.
Da wannan ne Dosara ya ke shawartar kafofin watsa labaran uku da su gaggauta janye rahotannin karya da suka wallafa a kan tsohon gwamnan cikin sa’a 24 ko kuma lamarin ya kai har gaban kotu.