
Tsohon Shugaban PDP Na Kasa Ahmad Mu’azu ya sauye sheka zuwa APC
Rahotonni sun nuna cewa tsohon shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon gwamnan jahar Bauchi, Ahmed Adamu Mu’azu, ya sauya sheka zuwa APC.
Daya daga cikin masu kare muradun shugaba Muhammadu Buhari a kafofin sada zumunta, Kayode Ogundamisi ne ya bayyana hakan a jiya Laraba 9 ga watan 2019 .
Tsohon shugaban PDP, Alhaji Adamu Muazu ya ajiye yakin neman zaben dan atakarar shugabancin kasar Najeriya karkashin inuwar jam’aiyyar PDP Atiku Abubakar ya sauya shekar zuwa APC.