Tsoron yaduwar corona ta sa a sallame masu yiwa kasa hidima

Hukumar yiwa kasa hidima ta Najeriya NYSC, ta garkame dukkanin sansanonin horas da masu yiwa kasa hidima dake fadin kasar ta Najeriya don gudun yaduwar annobar cutar ta Coronavirus wacce aka sauya wa zuna zuwa Covid 19 a tsakanin al’umma.

Premium Times ta ruwaito cewa  rukunin farko masu yiwa kasa hidima, wanda suka fara samun horo a sansanonin NYSC dake fadin jahohin na Najeriya ne a ranar 10 ga watan Maris, inda zasu kwashe kwanaki 21 a sansanonin,  sai dai kwanakin su 8 a ka dauke matakin gaggawa na sallamarsu, bisa tsoron kamuwa ta cutar.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More