
Wa kuke wa fatan samun nasara a Jahar Kano?
Kotun sauraran kararrakin zaben Gwamnan jahar Kano ta sanar da ranar Laraba 2 ga watan Oktoba 2019, a matsayin ranar da za ta yanke hukuncin sauraren kararrakin zaben da jam’iyyar adawa ta PDP tare da dan takarar Gwamnan jahar na PDP Abba Kabir Yusuf, suka shigar na kalubalantar nasarar da Gwamnan jahar Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya samu a zaben da aka gudanar na 2019.
Lauyan jam’iyyar APC Barrister Christopher Oshomegia, da na PDP Barista Bashir Yusuf, duk sun tabbatarwa wa neman labarai a yau Litinin 30 ga watan satamba shirin da kotun ke yi na yanke hukuncin wanda ya samu nasarar lashe zaben Gwamnan na jahar Kano wanda aka gudanar a watan faburairu na 2019.