Wacce shawara kuke da ita ga Adam Zango da Malam gama da laffuzan su?

Shahararren dan wasan fina-finan hausa Adam A. Zango ya karyata wani malami da ya yi ikirarin cewa jarumin yana neman mata yan kasa da shekara 20 da zummar tantance su domin ya sanya su a wani sabon shiryin fim dinsa wanda yace a yanzu haka ya jigine rubutun (script) a dalilin magangau da suke kaiwa suna dawowa.

A wani bidiyo da jarimin ya sanya a shafin sa wanda ya nuno wani malami yana huduba, ya ce jarumin ya fice daga masana’antar Kannywood ne saboda ba ya so hukumomi su tace fina-finansa da niyyar bin tsarin tarbiyyar addinin Musulunci.

Inda malamin ke cewa jarumin yana neman mata ‘yan kasa da shekara 20 domin ya sanya su a fim da zummar lalata tarbiyarsu da kuma hana hukumomin tace fina-finai gudanar da aikinsu.

Hakan ya sa Adamu kalubalantar malamin tare da yi masa “Allah-Ya-Sa” bisa zargin cewa ya masa kazafi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More