Wadanne kungiyoyi ne su kai nasarar samun tikin buga Gasar Zakarun Turai ta 2021/2022?

Bayan kammala manyan gasannin kwallon kafa guda biyar na Nahiyar Turai,wasu daga cikin manyan kungiyoyin, da kyar da jibin goshi, suka sami tikitin buga Gasar Zakarun Turai ta shekarar 2021/2022.
A gasar Firimiyar kasar ingila,kungiyoyin Chelsea da Liverpool sun sha da kyar wajen samun tikitin buga gasar ta Zakarun Turai, yayin ita ma Juventus da ke murza leda a Gasar Serie A ta kasar Italiya ta fuskanci mummunan barazar rasa tikitin buga gasar.
Yaya tsarin fid da rukunin gasar Zakarun Turai na kakar wasa ta 2021/2022 zai kasance?
Kungiyoyin da suka lashe gasar ta Zakarun Turai da wadda ta lashe gasar Europa League zasu kasance a matakin tukunya mai daraja ta daya ( Pot 1) . Wato dai ko Manchester City ko Chelsea, da kuma s one Manchester United ko Villarreal.
Villarreal za ta samu tikitin buga gasar Zakarun Turai idan ta doke United a ranar Laraba a wasan karshe na gasar Europa League.
Bayan wadannan kungiyoyi guda biyu da zasu kasance a cikin tukunya mai daraja ta farko, sauran kungiyoyin da za su kasance a tukunyar sune kungiyoyin da suka lashe manyan gasannin kasahen Nahiyar Turai na kasashen Jamani,Italiya,Ingila,Faransa, Sifaniya da Portugal. Wato kungiyoyin Atletico, City, Bayern, Inter, Lille da Sporting.
Kungiyar Zenit Saint Petersburg da ta lashe gasar Firiyar kasar Russia ita ma za ta kasance a tukunyar mai daraja ta daya idan Man City ta lashe gasar Zakarun Turai.
A tukunya mai daraja ta biyu kungiyoyin da suka hada da Real Madrid, Barcelona, Juventus, Paris Saint-Germain, Liverpool da Sevilla ne zasu kasance a cikin ta. Yayin da kungiyoyin Borussia Dortmund, Porto, Ajax da RB Leipzig suma ka iya kasancewa a tukunya mai daraja ta biyu ko ta uku.
Sauran kungiyoyin da suka samu tikitin buga gasar ta Zakarun Turai sune Atalanta, Besiktas, Dynamo Kiev, Club Brugge, AC Milan da Wolfsburg.
Wato dai za a iya samun rukunin da zai hada
Manchester City, Barcelona, Borussia Dortmund da AC Milan. Or what about ko Chelsea, PSG, RB Leipzig da Atalanta.
Sauran kungiyoyin da ka iya samun tikitin buga gasar bayan sun buga wasan share fage, sune

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More