Wanda mataki kuke ganin ya kamata a dauka game da abuda ya faru tsakinin sheikh Pantami da yan Kwankwasiyya?

Wani bidiyo da a yanzu haka ya karade kafafen shafukan sadarwar zamani na dauke da yadda wasu daga cikin mabiya Kwankwasiyya suka ci mutuncin fitaccen Malamin addinin Islama kuma Ministan mai ci gwamnatin yanzu wato sheikh Isa Ali Pantami.

Bidiyon na nuna   Sheikh Isah Ali Pantami, jami’an tsaro da kuma yaran Kwankwasiyya, inda yan Kwankwasiyyan ke yiwa  Sheikh Pantami ihun ”Ba ma yi”, wasu ma suna kokarin cafko shi yayin da jami’an tsaro ke kokarin kareshi.

Lamari  ya faru ne a ranar Talata 24 ga watan Satumba 2019 a filin sauka da tashin jirgin sama  na Malam Aminu Kano dake birnin Kano a daidai lokacin da Ministan ke kan hanyarsa ta komuwa Abuja daga Kano.

A daidai wannan  lokacin ne  su kuma wasu dalibai 242 da gidauniyar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta dauki nauyin karatunsu sun isa tashar jirgin da nufin tafiya zuwa Legas, inda daga can zasu wuce kasashen Indiya da kuma Sudan

Sanata Kwankwaso ya dauki nauyin dalibai masu darajar digiri lamba daya ne domin su karo karatun digiri na biyu a fannoni daban daban a jami’o’in kasar Indiya, daga ciki har da jami’ar Sharda, inda dalibai 234 zasu yi karatu a India, 8 kuma zasu yi a Sudan.

Kasancewar ministan babban malamin addini ne da yake amfanar da al’umma, bai hana neman yaga masa riga a titi ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More