Wanda mataki kuke ganin ya kamata a dauka gami da abun da ya faru tsakinin Ekweremadu da Kungiyar IPOB?

Wanda mataki kuke ganin ya kamata a dauka gami da abun da ya faru tsakinin Ekweremadu da Kungiyar IPOB?
 
Yan kabilar Igbo mazauna kasar Jamus ne dai suka gayyaci tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Sanata Ekweremadu da ya gabatar da kasida a taron ci gaba da kuma baje kolin al’adun kabilar Igbo a kasar Jamus.
Ana cikin wannan taro ne a birnin Nuremberg sai wasu “bata gari” da ake zargin ‘ya’yan kungiyar da ke fafutukar ganin yankin kudu maso gabashin Najeriya ya balle daga kasar, wato IPOB, suka kutsa cikin taron suka far wa Sanata Ike Ekweremadu.
 
Wani bidiyo da shafin Sahara Reporters ya wallafa ya nuna yadda wasu mutane suka rinka kulle-kucciya da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ta Najeriya.
An ga wasu na dukan sa, inda wasu kuma ke jifan sa tare da kokarin cire masa riga, kafin daga bisani ya samu ya shiga mota ya tsere, inda ita kanta motar sai da aka bi ta ana duka.
 
Su dai ‘yan wannan kungiya ta IPOB na zargin Sanata Ike Ekweremadu da hannu a “cibayan” da yankin kudu maso gabashin na Najeriya yake fuskanta musamman rashin yin katabus din manyan yankin wajen taimaka wa kungiyar ballewa.
 
Kungiyar IPOB, wacce aka haramta a kasar, ta dade tana sa kafar wando daya da jagororin yankin saboda kallon da suke yi musu na yi wa tafiyar kungiyar kafar ungulu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More