Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa ,Emmanuel Macron

Wani mutum a cikin taron mutane ya mari shugaban Faransa Emmanuel Macron a fuska yayin da yake magana da jama’a yayin ziyarar da ya yi a kudu maso gabashin Faransa a ranar Talata, bidiyon lamarin da aka yada a shafukan sada zumunta ya nuna.
Hoton bidiyon, wanda kafar watsa labarai ta BFM da ke da alaka da CNN ta nuna, ya nuna Macron yana tafiya zuwa ga shingen yana manne da hannun wani mutum a cikin taron yayin da ya fara gaisawa da masu kallo a kauyen Tain-l’Hermitage, a yankin Drôme na Faransa .
Mutumin, yayin da ya damke hannun Macron don su gaisa,ya mari Shugaban a gefen kuncinsa na hagu tare da yin kuwwa yana mai cewa ƙarshen “Macronie” yazo – kalma zambo da ake amfani da ita a cikin jaridun Faransa don nufin shugabancin Macron.
Cikin hanzari jami’an tsaro suka janye Macron daga wurin shingen.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More