Wannan ne zabe mafi muni a tarihin Najeriya – Atiku

A wani taron manema labarai da Alhaji Atiku Abubakar dan takarar jam’iyyar PDP ya gudanar a Abuja, ya bayyana cewa sakamakon babban zaben da aka bayyana ‘almara ce kawai’ kuma ba zai amince da shi ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi takarar shugabancin kasar ne a karkashin jam’iyyar PDP, inda ya sha kaye a hannun Shugaba mai-ci Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.
Atiku ya ce “a matsayina na dan Najeriya ina ganin wannan zaben na zamba da INEC ta gudanar ba shi da ingancin da zai samar wa ‘yan Najeriya shugaban kasa domin ba ra’ayinsu kenan ba”.
Ya kuma bayyana dalilin rashin amincewa da sakamakon kan cewa kuri’un da Buhari ya samu a wasu bangarorin kasar sun wuce kima, ciki har da jihohin kudu maso kudu da kuma na Arewa maso gabas wadanda yakin Boko Haram ya daidaita.
“A jihar Akwa Ibom misali, an samu raguwar yawan rajistar masu zabe da kashi 62% daga zaben shekarar 2015, hatta a inda rajistar masu zaben da kuma wadanda suka karbi katin jefa kuri’a take da yawan gaske a zaben da ya gabata.
‘Wannan kuskuren an kuma maimaita shi a jihohin da PDP ke da karfi kamar Delta da Rivers da Abia da kuma Benue, inda a Borno kuma aka samu karin kashi 82% na rajistar masu zabe. Kai ka ce rashin tsaro kamar bai wa a gare su wurin yawan kuri’a”.
Bisa wannan dalilki ne kuma Atiku Abubakar ya ce ya yi watsi da sakamakon zaben tare da bayyana cewa har yanzu bai fitar da rai ba.
Atiku ya ce wannan zaben shi ne mafi muni da aka taba gudanarwa a Najeriya a cikin shekara 30.
“A shekara 30 da na yi a harkar siyasa wannan shi ne zabe mafi muni da na taba gani a Najeriya.
“Kuma na gaya wa Janar Abdussalami Abubakar lokacin da ya kira cewa hatta zabukan da gwamnatocin soja suka gudanar ya fi shi inganci.”
Yadda zaben yake?
Duk dan takarar da ya samu kuri’un da suka fi yawa, idan dai har ya samu kaso 25 na kuri’un da aka kada a jihohi 24 daga jihohi 36 na kasar.
‘Yan takara 73 ne suke neman kujerar shugabancin kasar amma fafatawar ta fi zafi tsakanin ‘yan takarar jam’iyyu biyu.
Taken Jam’iyyar shugaba mai ci, Muhammadu Buhari shi ne ‘Next Level’ wato kai Najeriya zuwa matakin ci gaba

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More