Wasannin Kwallon kafa

Dan wasan gaban Manchester United da kasar Ingila Marcus Rashford mai shekaru 21 zai sabunta kwantiragensa da kungiya kan kudi fam miliyan £78, a cewar jaridar Mirror.

Tsohon kocin Chelsea Antonio Conte na da niyyar zama sabon kocin Inter-Milan idan kungiyar za ta maida dan kasar Italiyan kocin da yafi kowanne koci yawan albashi a gasar SerieA, in ji Mail.

Da yiwuwar dan wasan tsakiyar Real Madrid da kasar Colombia James Rodriquez mai shekaru 27 zai koma Juventus,sa’ad da ake tsammanin komawar dan wasan gaban Chelsea Eden Hazard Bernabeu, a cewar Marca.

Yayin da Telegraph ke cewa dan kasar Belgium din mai shekaru 28 zai ki amincewa da sake sabunta kwantiragensa da Chelsea koda kuwa kungiyar za ta tsaurarawa Real Madrid wajen daukarsa.

Dillalin Gareth Bale mai shekaru ya ce dan wasan kasar Wales din mai shekaru 29 na farin cikin zamansa a Real Madrid,kuma dan wasan gefen bashi da burin komawa Gasar Firimiya da taka leda, in ji Mirror.

Yan wasan Manchester United ka iya fuskantar ragewar kudadensu da kaso 25% muddin suka gaza samun gurbin doka Gasar Zakarun Turai. Kuma da yiwuwa Real Madrid zata mika tayin daukar Paul Pogba mai shekaru 26 idan United din ta koma doka Gasar Europa League, in ji jaridar Sun.

Arsenal da Tottenham na da sha’awar daukar dan wasan tsakiyar Inter-Milan da kasar Croatia Ivan Perisic mai shekaru 30, a cewar Corriere dello Sport.

Ita ko kafar Manchester Evening News ruwaitowa ta yi cewa dan wasan gaban kasar Ivory Coast Wilfred Zaha mai shekaru 26 ya ce zai ci gaba da zama a Crystal Palace duk da rahotannin dake alakanta shi da komawa Manchester United.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More