Wasannin Kwallon kafa: rade-radi

• Manchester United ta kintsa tsaf don mika tayin FAM miliyan £120 ga Juventus kan daukar dan wasan gaban kasar Argentina Paulo Dybala, mai shekaru 25, idan dan wasan gaban kasar Belgium Romelu Lukaku mai shekaru 25 ya bar Old Trafford a karshen kakar wasa ta bana, a cewar Sun.

• An fara tattaunawa tsakanin AC Milan da mai tsaron ragarta Gianluigi Donnarumma mai shekaru 20 kan batun sabunta masa kwantirage. Milan dai na son tsawaita kwantiragen golan har zuwa 2023, a cewar Calceomercato.

• Dan wasan tsakiyar Ajax Frenkie de Jong mai shekaru 21 ya ce Barcelona ta fada masa cewa ya cire Madrid daga Gasar Zakarun Turai. Dan wasan kasar Netherlands din dai zai koma kungiyar zakarun Gasar Laliga a karshen kakar wasa ta bana,in ji Evening Standard.

• Ita ko Reuters cewa ta yi Andres Iniesta ya ja ra’ayin dan wasan tsakiyar Spain Sergi Samper mai shekaru 24 ya bar Barcelona ya koma kungiyar Vissel Kobe da ke kasar Japan.

• An bawa magoya bayan Real Madrid damar zabar yan wasan da kungiyar ya kamata ta sayar,da kocin da kungiyar ya kamata ta kawo, a cewar Marca.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More