Wasu yan majalisan Najeriya sun amince da shirin tunbuke mataimakin gwamnan Kogi

Majalisar Dokokin ta jahar Kogi ta gabatar da kudiri na neman tsige mataimakin gwamnan jahar Kogi, Elder Simon Achuba, kan zargin sa da rashin da’a da aikata ba daidai ba.

Shugaban masu rinjaye a majalisar ta Kogi, Abdullahi Belle (dan majalisar da ke wakiltar Ajaokuta a jami’iyyar APC) shi ne ya karanta wata takardar koke da korafi da a ka gabatar a gaban zauren majalisar a zaman da ta yin a jiya Laraba 7 ga watan Agusta 2019, inda takardar ke zargin mataimakin gwamnan da nuna rashin da’a a cikin kwanakin wayansu kwani.

Shugaban masu rinjayen ya shaida cewar ’yan majalisu 21 daga cikin 25 da jahar ta ke da su, sun sanya hannu ne kan zargin da a ke yiwa mataimakin gwamnan da cewar a ’yan kwanakin nan wasu kalaman mataimakin gwamnan babu da’a ko ladabi a cikinsu wadanda su ke da bukatar a gudanar da bincike na tilas a kai.

Ya karanta sashen doka na 188 da ke kundin tsarin mulkin kasa na 1999 hadi da fatan cewar majalisar za ta kaddamar da fara bincike a kan zarge-zargen da ke kan mataimakin gwamnan Achuba wadanda ya aikata.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More