Wata mata ‘yar Afirka ta Kudu ta haifi jarirai goma, ta karya tarihin kundin Guinness Record

Wata mata ‘yar Afirka ta Kudu ta haifi jarirai 10, wanda hakan ya ba ta damar karya tarihin macen da ta fi kowacce haihuwar yaya da yawa a lokaci guda a duniya da wata ‘yar kasar Mali Halima Cisse ,wacce ta haifi yara tara a Morocco a watan Mayu, ke rike da shi.

A cewar kafafen yada labaran cikin gida na Afirka ta Kudu, Gosiame Thamara Sithole, mai shekara 37, an yi mata tiyatar haihuwa domin ta haifi yara maza bakwai da mata uku lamarin da ya sanya ta zama wacce ke rike da kambum Guinness Record na mafi yawan yaran da mace daya ta haifa a lokaci daya.

Rahotannin sun ci gaba da nuna cewa Sithole da mijinta Teboho Tsotetsi suna tsammanin jarirai takwas saboda awon da aka yi mata ya nuna yaya takwas za ta haifa sakamakon sakamakon rashin iya ganin jarirai biyun da injin awon na masu ciki ya yi.

“Na kadu da cikin na. Ya kasance da wahala da farko. Nayi rashin lafiya. Ya kasance mini da wuya.  Har yanzu yana da wuya amma na saba da shi yanzu. Ba na jin zafi kuma, amma har yanzu yana da ɗan tsauri. Ina dai addu’ar Allah ya taimakeni ya sadar da dukkan yarana cikin koshin lafiya, kuma ni da yarana mu fito da rai. Zan yi farin ciki da hakan, ”in ji Sithole kamar yadda ta fada wa kafafen yada labaran kasar.

Da yake magana da Pretoria News, Tsotetsi ya ce Sithole ta haifa musu tarin farin ciki makonni 29 da samun cikin ta.

Sithole wacce ke da yan tagwaye ‘yan shekaru shida ta fadawa manema labarai haihuwar jarirai goman rijis a daren ranar Litinin, tana mai cewa tana mai cike da murna.

A watan Mayu, wata mata ‘yar kasar Mali ta haifi yaya tara a Maroko, wanda hakan ya karya tarihin da wata Ba’amurkiya, Nadya Suleman ,wacce ta haifi jarirai takwas a shekarar 2009.

Rahotanni sun nuna cewa sau biyu ne kawai aka taba samun haihuwar yara tara a lokaci guda tun daga shekarun 1970, amma jariran duk sun mutu cikin a rana daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More