Watsa min acid ya kara min kwarin gwiwa ne – Nura M Inuwa

Shahararren mawakin fina-finan Hausa Nura M Inuwa, ya bayyana yadda ya samu kwarin gwiwa bayan watsa masa acid din da akayi bayan wasu yana shekaru da suka wuce.

Mawakin ya bayyana hakan ne a wata hirar da ya yi da BBC a kwanakin baya da suka wuce.

Nura ya ce abin da ya same shin ya kara masa son jama’a ne, maimakon  jama’ar su guje shi.

Inda ya kara da cewa ya  yarda  Allah ne mai yi kuma yayi masa, domin ya saka wa mutane son sa tare da wakar sa acikin zukatan su.

Nura M. Inuwa yace an yaudare shi ne da sana’ar sa gurin gayyatar shi da yaje yayi waka da haka ne aka samu damar watsa masa Acid din, sannan watsa masa Acid din ne ya zama sanadiyyar sanya tabarau da yake yi.

A karshe  yace sanya tabarau din ya  zama shaidar Nura M. Inuwa, domin idan kaga Nura ba tabarau to ba Nura M. Inuwa bane.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More