Wulakancin da Barcelona ta yi mini ya sa ni kuka kafin komawa ta Atletico Madrid – Luis Suarez

Luis Suarez ya ce yadda Barcelona ta wulakanta shi ya sa ya yi ta zub da hawaye kafin ya tafi Atletico Madrid.
Dan wasan na Uruguay ya bar Barcelona a watan Satumba bayan ya shekara shida yana murza mata leda kuma ya ce an hana shi yin atisaye da sauran ‘yan wasan kungiyar kafin ya tafi.

“Na sha matukar wahala a wancan lokacin. Na yi kuka saboda halin da na tsinci kaina a ciki,” a cewar Suarez, mai shekara 33.

“Na fi jin zafin yadda ake gudanar da lamura, saboda dole mutum ya amince da abin da ya same shi.”

Suarez ya je Barcelona daga Liverpool a kan £74m a 2014 kuma ya kasance dan wasa na uku da ya fi ci mata kwallo
inda ya zura kwallaye 198.
Ya taimaka mata wajen lashe Kofin La Liga hudu, Kofin Copa del Reys hudu, Kofin Zakarun Turai daya da kuma Kofin Gasar La Liga ta Duniya guda daya a 2015.

Ya ci kwallaye 21 a kakar wasa ta 2019-20 – kuma wadannan su ne kwallaye mafi kankanta da ya zura a cikin shekara shida da ya kwashe a kungiyar.

Atletico ta biya abin da bai wuce euro 6m kan Suarez.
“Ban yarda da sakon kungiyar ba cewa suna nema mani mafita,” in ji Suarez, wanda ya zura kwallaye biyu a wasanni
uku da ya buga wa Atletico.

“Ba kowa ne ya san abin da ya faru ba amma abu mafi muni shi ne da na tafi wurin atisaye amma aka kai ni wani waje nadaban da na sauran ‘yan wasa.

“Matata ta ga irin bakin cikin da na fada a ciki kuma tana so na rika murmushi don haka da dama ta zo ta tafiya Atletico ban yi wasa ba kawai na tafi.”

A wancan lokacin, Lionel Messi ya ce Luis Suarez ya cancanci a yi masa karramawar da ta fi wadda Barcelona ta yi masa da zai bar kungiyar kodayake ya ce a halin yanzu “babu abin da yake ba ni mamaki” kan abin da aka yi wa dan wasan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More