Ya kamata Legas, Oyo Su Biya Diyya – SERAP

Kungiyar SERAP mai hankoron ganin an tabbatar da adalci a tsakanin al’umar a Najeriya ta yi kira ga gwamnatocin jahohin Legas da Oyo, da su dauki matakan gaggawa domin ganin an daina danne  hakkin bil Adama.

Kungiyar ta SERAP, ta yi kiran ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter inda ta nemi jahohin da su biya diyya ga iyalan da rushewar gidaje ya  shafa a jahohin.

“Ya kamata gwamnan jahar Legas, Akinwumi Ambode da takwaran aikinsa na Oyo, Abiola Ajimobi, su dauki matakan gaggawa wajen tabbatar da cewa an yi wa iyalan adalci, wajen ganin a biya kowannan su diyya.

Haka zalika sanarwa ta kuma nemi gwamnatocin da su tabbatar da cewa, irin wadannan hadurra ba su sake aukuwa ba.

A makon da ya gabata wani bene mai hawa uku ya rushe a jahar ta Legas inda ya halaka mutum akalla 20 ciki har da daliban firaimari da makarantarsu ke bene na uku.

Sannan  cikin makon da ya gabata, wani gini shi ma ya rushe a birnin Ibadan na jahar Oyo da ba ta da nisa tsakanin su da  jahar ta Legas.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More