Yadda Aisha Buhari ta roki gafarar iyalanta ta ma yan Najeriya

Uwargidan  shugaban Najeriya Aisha Muhammadu Buhari ta nemi afuwar ya yanta da kuma daukacin yan Najeriya kan duk wani abin kunya da bidiyon da aka gan ta tana fada a ciki ya jawo, wanda ya yadu a makon da ya gabata.

A cikin bidiyon dai an ji Aisha Buharin tana ta bambamin fada a harshen Turanci, duk da dai ba a nuna fuskarta ba.

A ranar da ta dawo daga Ingila ne  ta tabbatar da cewar ita ce a bidiyon amma yar didan  Mamman Daura Fatima ce ta dauke ta tare da yi mata dariya a gurin dauka.Hakka kuwa Fatima bata musanta cewar ita ta dauki wannan bidiyon ba.

Aisha Buhari ta nemi  afuwar ne a ranar Laraba 16 ga watan Oktoba 2019 a lokacin da ta karbi bakuncin matan gwamnonin kasar 36 a fadar shugaban kasar, kamar yadda wata sanarwa da mai taimaka mata kan yada labarai Suleiman Haruna ya fitar.

Sannan  ta wallafa sakon ban hakurin a shafinta na Instagram.

wannan shine sakon da ta wallafa a shafin nata:

“Na yi farin cikin wanan ziyara da matan gwamnoni da matar shugaban majalisar dattawa da ta majalisar dokoki da matan ‘yan majalisar suka kawo min don yi min barka da dawowa.

Ina so na yi amfani da wannan damar wajen jinjina musu kan aiki na gari da suke yi a jihohinsu tare da hadin gwiwar shirina na Future Assured.

“Ina kuma ba su shawara da kar su bari wani abu da ake yadawa a kafafen sada zumunta ya dauke musu hankali ko wani abu daban na kafafen sadarwa.

“Ina amfani da wannan damar don neman afuwa kan abin kunyar da watakila na jawowa ‘ya’yana da iyalaina da dangina da ma ‘yan Najeriya baki daya da kuma kujerar da nake wakilta kan bidiyon da ya bulla wanda ya yadu tamkar wutar daji.

“Gaba dai gaba dai Najeriya.”

Sannan kuma tayi godiya ga maigidanta wato shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari kan sabbin mukamai shida da ya yi wa ofishinta na masu taimaka mata na musamman.

Wannan sune sabbin ma’aikatan da Aisha Buhari za tayi aiki dasu:

  • Muhammed Albishir – Mai taimaka mata ta musamman kan Kungiyar Matan Shugabannin Kasashen Afirka kan Ci gaba OAFLAD.
  • Mairo Almakura – Mai taimaka mata ta musamman kan Kungiyar Matan Shugabannin Kasashen Afirka AFLPM.
  • Wole Aboderin – Mai taimaka mata na musamman kan Kungiyoyi Masu Zaman Kansu NGOs
  • Zainab Kazeem – Mai taimaka mata ta musamman kan Harkokin Cikin Gida da Tarukan Nishadi
  • Barista Aliyu Abdullah – Mai taimaka mata na musamman kan Harkokin Yada Labarai
  • Funke Adesiyan – Mai mataimaka mata kan Harkokin Cikin Gida da Tarukan Nishadi.

Kafin sanarwa ta fita, Aisha Buhari ta bayyana wa  manema labarai godiyar ta ga mijinta Shugaba Buhari a ranar da ta dawo   kan bayar da sabbin mukamai har shida na ofishinta.

Matar gwamnan Bornon Hajiya Falmata Zulum ce ta jagoranci matan gwamnonin arewacin Najeriya yayin da matar gwamnan Edo Betsy Godwin Obaseki ta jagoranci matan gwamnoni daga kudu.

Hajiya Falmata ta ce sun je fadar shugaban ne don yi wa Aisha Buhari maraba bayan da ta shafe tsawon lokaci ba ta kasar, dannan kuma su kara tabbatar da goyon bayansu kan ayyukanta.

Sauran matan da suka halarci taron sun hada da matar mataimakin shugaban Najeriya Dolapo Yemi Osinbajo da Maryam Ahmed Lawan matar shugaban majalisar dattawa da kuma Salamatu Femi Gbajabiamila.

A nata bangaren Aisha Buhari ta sha alwashin gina sakatariyar yanki ta Kungiyar Matan Shugabannin Kasashen Afirka AFLPM.

A shekarar 1995 ne aka kirkiri AFLPM a babban taron Beijing na kasar China.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More