Yadda aka binne gawar sanata Zarewa

Gwamnan jahar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje tare da tawagar sun karbi gawar Marigayi Sen Isa Yahaya Zarewa a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano wanda Allah yai wa rasuwa a birnin tarayyar Abuja, a ranar Litinan 4 ga watan Nuwamba 2019, daga bisani kuma akayi janaizar za a birnin Kano da misalin karfe 2 na rana a gidan sa dake kan titin Yahaya Gusau

Sanata Isa Yahaya Zarewa a garin Zarewa ya rasu yana da shekaru 61,kuma dan karamar hukumar Rogo dake jahar Kano ne.

Marigayi Zarewa ya wakilci jahar Kano ta kudu a majalisar dattijai daga shekarar 1999 zuwa 2003 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, sannan ya yi gwagwarmayar siyasa a jam’iyyu da dama da suka hada da SDP, PDP, APC da jam’iyyar PRP, wacce ya koma bayan ya rasa tikitin takarar Sanata a jam’iyyar APC a zaben fidda ‘yan takara a shekarar 2018.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More