Yadda aka gano gawar Fahim Saleh   mai kamfanin Gokada a New York

Yan sandan New York sun sanar da cewa an kashe mai kamfanin Gokada, Fahim Saleh,  a wani gida da ke Manhattan na birnin.

Wakilin BBC Kunle Falayi ya ruwaito cewa yar uwar Mista Saleh ce ta gano gawarsa ranar Talata.

Kakakin Yan Sandan na New York ya ce bayan an kashe shi, an kuma daddatsa gawarsa da wani zarto mai amfani da lantarki wanda Yan sandan suka taras a kusa da gawar mamacin.

Mista Saleh ya kafa kamfanin Gokada, kamfanin da ke samar da baburan haya a Najeriya cikin birnin Legas a shekarar  2018,  wanda ya kawo sauyi ta fuskar fasahar zamani ga harkar sufuri a babban birnin kasuwancin Najeriya.

Jarin kamfanin ya kai dala miliyan 5.3 a lokacin da ya fara aiki cikin watan Yunin 2019.

Kamfaninsa ya sanar da kisan da aka yi wa dan kasuwan a Twitter, kuma labarin ya girgiza Yan kasuwa masu yawa – musamman na bangaren fasahar sadarwa.

A watan Fabrairun 2020, Mista Saleh ya mayar da kakkausan martani cikin wani bidiyo da ya fitar, bayan da gwamnatin jahar Legas ta dakatar da amfani da babura a wasu sassa na jahar.

Wannan matakin na gwamnatin Legas ya tilasta wa kamfanin nasa ya koma amfani da baburan domin jigilar kaya a madadin daukan fasinja.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More