Yadda aka kama wani matashi da bam a cikin coci a jahar Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jahar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wani matashi dauke da ababen fashewa a cikin jakarsa, a Cocin Living Faith da ke Unguwar Sabon Tasha, daidai lokacin da mabiya addinin Kirista ke gudanar da ibadarsu a ranar Lahadi.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jahar DSP Yakubu Abubakar Sabo ya shaida wa BBC cewa sunan matashin Nathaniel Samuel, kuma ya shiga cocin ne dauke da wata jaka a matsayin wanda ya je ibada.

DSP Yakubu ya ci gaba da cewa “Sai ya ajiye jakar a kan kujera daga nan ya sulale ya shiga bandaki, ya kai fiye da sa’a guda bai fito daga bandakin ba.

“Hakan ne ya ja hankalin mutanen da ke cikin cocin, sannan suka lura cewa ga jakar a ajiye ita kadai kan kujera har zuwa lokacin.

Daga nan ne sai mutane suka sanar da jami’an ‘yan sandan da ke cocin wadanda suka je yin aikinsu, inda su kuma suka shiga suka tilasta masa fitowa daga bandakin, sannan suka sa shi ya bude jakar,  da suka  duba ne suka tarar da kayayyakin da ake hadawa wajen tayar da wasu abubuwa,” a cewar mai magana da yawun ‘yan sandan.

Amma jami’in ‘yan sandan ya ce matashin bai daura abubuwan a jikinsa ba sai dai a jakarsa kawai kamar yadda aka gano.

Rundunar ‘yan sandan ta ce matashin yana tsakanin shekara 30 ne zuwa 32 kamar yadda ya sanar musu, “sannan kuma alamu sun nuna cewa yana cikin hayyacinsa.”

DSP Yakubu ya ce a halin yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin, “kuma za mu yi wa manema labarai karin bayani nan gaba,” in ji shi.

Sai dai ya tabbatar da cewa bayan faruwar lamarin mutane sun ci gaba da al’amuransu na yau da kullum cikin kwanciyar hankali a nan Unguwar Sabon Tasha, sannan masu ibadar da ke cikin cocin ma sun kwantar da hankalinsu.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More