Yadda ake sayar da katin zabe a Kano

A ranar Asabar 23 ga watan Maris ne hukumar hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta shirya gudanar da zabukan gwamna a wasu yankuna da aka soke na wasu jihohin kasar.

Sai dai wata babbar matsala da tun farko aka bankado ita ce yadda ake cin kasuwar saye da sayar da kuri’u ba tare da kakkautawa ba.

Tuni dai hukumar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta kama wasu da take zargi da laifin sayar da kuri’un, kuma ta ce tana iyakar bakin kokarin ta wajen hana irin wannan dabi’a.

To sai dai wakilan BBC Yusuf Yakasai da Halima Umar Saleh wadanda suka je Kano domin dauko shirye-shiryen zaben, sun gano ta karkashin kasa yadda ake wannan sana’a ta saye da sayar da katunan zabe.

Sun gano cewa mata na daga cikin wadanda aka fi tunkara domin sayen katin zabe a wurin su.

Kuma sau da dama akan yi amfani da dubaru, kamar wasu kalmomi da ba za a iya ganewa kai-tsaye ba, wajen cinikayyar katin zabe.

A misali, wata mata da ta tunkari Halima Umar Saleh domin sayar da katin zabenta, ta ce wa Halima ‘ya kamata ki sayi buta domin a bayar sadaka a masallaci’.

Sannan ta kara da cewa ‘akwai buta akwai kuma buta (voter)’.

Bayanai sun nuna cewa ja,i’an tsaro na shiga irin wadannan unguwanni da za a sake gudanar da zabukan domin hana sayar da katin zaben.

Sai dai kuma irin wadannan mutane masu son sayar da kuri’unsu kan yi mahada da masu son sayen kuri’un a wasu unguwanni na daban, domin gudun kada a kama su a lokacin da suke kokarin sayar da kuri’un nasu.

Ko a lokacin zaben gwamnoni da ya gabata, wasu hotuna da bidiyo da ke nuna yadda ake amfani da kudi wajen sayen kuri’a sun rinka yawo a shafukan sada zumunta.

Hukumomin da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati na EFCC da ta yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC sun bayyana sayen kuri’a a matsayin laifin cin hanci.

Ko a wani taron wayar da kai da ICPC ta gudanar a watan Disambar 2018 ta ce sayen kuri’a zamba ce a dimokradiyya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More