Yadda alkali ya gargadi Maina a zaman na Kotu

Babban alkalin da ke jagorantar Abdulrasheed Maina, wato Justice Okon Abang, ya gargadi shi da cewa kotu ba zata cigaba da lamuntar ‘wasan kwaikwayo’ ba a lokacin zaman kotun na 21 ga watan Nuwamba 2019.
 
Alkalin ya sanar da hakan ne yayin duba bukatar dage shari’ar saboda halin rashin lafiyar da Maina ke ciki. Kuma zamansa a tsare, na da alaka da halin da yake ciki.
Tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa Abdulrasheed Maina na fuskantar shari’a ne a kan zargin laifuka 12 da suka hada da almundahanar kudi tare da boyewa don gujewa hukunci da ake masa. Dan sa Faisal na fuskantar shari’a a gaban kotun da Maina ke fuskantar tasa a kan laifuka mabanbanta har uku.
 
A yayin da kotun ke cigaba da sauraron martanin lauyoyin dayan bangaren, jami’in tsaro da ke aiki da kotun ya tunkari kotun don sanar da alkalin yadda ake watsa wa Maina ruwa, yayin da ya ke zaune a wajen zaman da ke karshen kotun.
 
A wannan lokacin ne lauyan Maina, Francis Oronsaye, ya sanar da alkalin cewa, ya na da niyyar mika bukata ga kotun da ta bar wanda yake karewa ya sha maganinsa, sai baya son a ga kamar yana son dakatar da zaman kotun.
 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More