Yadda Almajirai da dama suka daina bara dalilin bude sabon gidan abincin “Naira 30”

A kwanak0in baya ne ministan harkokin noma wato Sabo Nanono, ya bayyana cewa N30 ta isa mutum ya ci abinci ya koshi a Kano, inda fadar hakkan ta jawo cece-kuce a Kano.

Bayan faruwar al’amarin ne yasa wani mutum ya bude gidan sayar da abinci na N30 din a Kano.

Wasu mutane a jahar  Kano sun bayyana cewa sabon gidan abincin yasa yawan barar da almajirai ke yi a kan hanya ya ragu sosai, dalilin bude gidan abincin a unguwar Sani Mainagge.

Wayanda ke makwabtaka da gurin sun dana dora sanwa sakamokon hakkan.

Mai gyaran Rediyo ya samu karfin giwa inda shi ma ya bude gidan abincin na “Naira 30”.

Legit ta rawaito cewa, Haruna Injinya  mai gidan sabon abincin naira 30 ya kara da cewa makotan nasa kan turo yara biyar da Naira dari da hamsin domin sayan abinci, kuma a rana yana dafa shinkafa buhu daya, wake rabin buhu da garin kwaki buhu daya. Ya kara da cewa wasu na zuwa gidan abincin domin saye a rabawa mabukata.

Sannan mai dakin Haruna wato Hajiya Sadiya Saidu ,ta ce hatta Almajiran unguwar na zuwa sayan abincin na “Naira 30”. Inda yasa suka daina bara sai dai su nemo naira 30 domin sayan abincin.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More