Yadda bata gari suka afkawa Oshoimhole a Benin

Rikicin da ya dabaibaye majalisar dokokin Jahar Edo, zai iya fadawa cikin wannan sabuwar gwamnatin, a sakamakon yanda ake zargin zauna gari banza da ake zargin cewa magoya bayan gwamnan jihar ne suka kaiwa Mista Seidu Oshiomhole, wanda kani ne ga shugaban jam’iyyar ta APC na kasa Mista Adams Oshiomhole hari a Benin.

Batagarin, sun kai harin kan Oshiomhole a ranar Talata, tare da wasu ‘yan majalisun jahar  guda 14

A yadda  hasheshen suka nuna  yan majalisun suna cikin gudanar da wani taro ne a wajen da ba a bayyana ba, kwatsam  zauna gari banzan suka kai musu hari wanda  ake zargin  da sa hannu gwamnatin jahar a harin da yan bata garin suka kai musu.

A Yadda sanarwar ta bayyana  taron ya samo asali ne da kaddamar da wakilai tara na sabuwar majalisar ne da aka yi a ranar Litinin da tsakar dare, da kuma zaben da ya biyo baya na Frank Okiye, a matsayin Kakakin majalisar Jahar.

In za a iya tunawa, tara daga cikin ‘yan majalisun jahar su 24 sun yi zama inda suka zabi Kakakin majalisar a bisa abin da za a iya kwatanta shi da mafarin rikici a cikin jahar.

Rikicin da ke faruwa a cikin majalisar dokokin jahar, ba zai rasa nasaba da sabanin da ke tsakanin Gwamnan jahar, Godwin Obaseki da kuma wanda ya gabace shi, Adams Oshiomhole

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More