Yadda dokar mafi karancin albashi zata fara aiki

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da kwamitin shirya yanda za a fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira 30,000.

Kimanin wata guda da shugaban kasa Buhari ya sanya hannu a kan dokar.

Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dakta Chris Ngige, ne ya fadi hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a gidan Talabijin kan yaushe ne za a fara biyan sabon mafi karancin albashin.
Sai dai bai bayyana yaushe ne gwamnatin za ta fara biyan sabon mafi karancin albashin ba, amma dai ya ce za a biya ariya a duk lokacin da aka fara biyan sabon mafi karancin albashin.
Ya ce, har yanzun akwai sauran matakan da suka kamata a bi kafin fara biyan sabon mafi karancin albashin, duk da cewa an sanya hannu a kan dokar.

Hukumar kula da albashi da kudaden alawus ya kamata ta yi aikinta a kansu kafin a fara biyan sabon mafi karancin albashin,” in ji Ministan. Ya ce, kwamitin da gwamnatin ta kafa ya kunshi Ministoci Bakwai ne, a inda shugabar ma’aikata na kasa, Winifred Oyo-Ita, take a zaman shugabar kwamitin.
Ministan ya ce, kananan ma’aikata na can kasa wadanda suke aiki a gwamnati ko a kamfanoni masu zaman kansu su ne za su kwashi albashin Naira 30,000, kamar yanda dokar ta tanada. Sai dai ya ce, ga ma’aikatan da albashin su yake sama da sabon mafi karancin albashin, za su sami kari ne a daidai matakan da suke a kai daga sama zuwa kasa.
Ngige, ya kara da cewa, sauran hukumomin gwamnati za su fitar da takardun doka kwanan nan a kan karin da aka samu.
A yanzun haka dai, shugaban kungiyar kwadago ta NLC, Mista Ayuba Wabba, ya nuna damuwarsa a kan jan kafar da ake yi wajen fara aiwatar da dokar ta sabon mafi karancin albashin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More