Yadda EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamna Filato a Kotu

Hukumar  yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jahar Filato Jonah David Jang da kuma Yusuf Pam wanda tsohon mai ajiya da bayar da kudi a ofishin sakataren gwamnatin jahar.

Hukumar ta gurfanar da su ne gaban Mai Shari’a C.L Dabup a kotun jahar ta Filato kan zarge-zarge 17.

Hukumar ta EFCC na zarginsu ne da almundahanar kudaden jahar da suka kai naira biliyan 30.

Tun a baya dai, an taba kai wannan karar a gaban Mai Shari’a Longji wanda kafin ya yi ritaya daga alkalanci a 31 ga watan Disambar bara, ya soke bahasin wadanda ake zargin inda suke cewa ba su aikata laifin almundahana ba musamman kan batun kudaden kanana da matsakaitan masana’antu da Babban Bankin Najeriya ya ba jahar da kuma na hukumar SUBEB da ake zargin sun karkatar.

Sai dai wayanda  ake zargin dai sun ki amincewa da laifukan da ake zarginsu da aikatawa, bayan haka lauyan da ke karar mutanen biyu ya bukaci kotun ta saka ranar fara shari’ar.

Lauyoyin da ke kare wayanda ake tuhuma  sun bukaci a bayar da belin wadanda suke karewa inda suka roki kotun ta tsaya kan belin da Alkali Longji ya bayar a baya.

Mai Shari’a Dabup ta bayar da beli ga wadanda ake zargin kan hujjojin Alkali Longji.

Kuma ta  bukaci masu tsaya musu da su cika takardu idan suna so su ci gaba da tsaya musu, tare da bada kwanaki uku domin cika sharuddan belin.

Kotu ta saka  26 zuwa 28 ga watan  Mayu 2020 a matsayin ranar fara shari’ar.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More