Yadda farashin man fetur ke tangal-tangal a Najeriya

Tun bayan kara farashin man fetur da gwamnatin Najeriya ta yi daga naira 133 zuwa 138.62 ko wacce lita daya, farashin man yake ta tangal-tangal a gidajen man kasar.

Kamfanin NNPC ya raba wata sanarwa ga masu kamfanonin man da masu dakon man, wadda ke dauke da sanarwar karin da aka samu.

Hakan dai ya sanya mafi yawan kamfanin dakwon mai irinsu DAFMAN da IPMAN sanar da karin farashin mai ga mambobinsu.

IPMAN ya ba da sanarwar duk wasu manbobinsa su sayer da man kan naira 150 ko wacce lita daya.

Wasu gidajen man sun kara nasu farashin,inda a gefe guda kuma, wasu kalilan sun yi na su karin amma bai kai wanda IPMAN ta ba da sanarwar mambobinta su yi ba.

 A watan Yuni sai da gwamnatin Najeriya ta kara firashin man fetur daga N140.80 zuwa N143.80 a duka kan lita guda, sannan a  farkon watan Afrilu 2020, gwamnatin ta sanar da ragin firashin man zuwa N123.50 a duk lita guda, lokacin da ake tsaka da faduwar farashin man a kasuwar duniya saboda annobar Coronavirus.

Sama da shekaru 20 firashin mai bai taba zama daidai ba a Najeriya. Wani lokaci ya hau wasu lokutan kuma a samu ragi.

Ku garzaya safin mu na facebook #OakTVHausa don ganin hotunan gidajen man a yau.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More