Yadda Gobara ta kama gidan su Obasanjo

 

Rahotanni daga jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya na cewa an yi gobara a gidansu tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo da ke Ita-Eko a Abeokuta.

Wani ginin wajen ajiya ya kone kurmus,  kamar yanda cewar shugaban kwana-kwana na jahar, Fatai Adefala ya shaida wa jaridar Vanguard.

Wani dangin tsohon shugaban kasar ya shaida wa jaridar TheCable cewa lamarin ya faru ne ranar Laraba da misalin karfe tara na dare, ko da yake gobarar ta shafi bangaren da matasa maza ke kwana ne kawai.

“A gidan ne mahaifan Obasanjo suka yi rayuwarsu har suka rasu. Tsohon gida ne. Ba shi ne babban gidan da Obasanjo ke ciki ba,” in ji mutumin.

Ya kara da cewa tuni aka kashe gobarar.

BBC ta rawaito cewa rahotanni sun ce Cif Obasanjo ba ya Najeriya lokacin da lamarin ya faru, kuma yana kan hanyarsa ta komawa gida daga taron kasashen Afirka da ya halarta a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia.

Jami’an kashe gobara a birnin Abeokuta na jahar Ogun, sun ce sun yi kokari sun kashe wutar da ta tashi a harabar gidan su tsohon shugaban kasar tun kafin ta kai ga cikin gidan.

Gidan mai hawa da dama harabar duk ta kone, amma kuma ainihin ginin gidan wutar ba ta ci shi ba.

Har yanzu ba a kai ga ga gano musabbabin tashin wutar ba, amma kuma ganau sun ce ba mamaki daga matsalar lantarki ne.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More