
Gobara ta kashe mutane 3 a Kano
Rundunar ‘yan sansan jahar Kano ta tabbatar da rasuwar mutum uku da suka hada da miji da matarsa da ‘yarsu sakamakon gobarar da ta afku a gidansu da ke Gayawa Tsohowa a karamar hukumar Ungogo.
Mai magana da yawun hukumar kwana-kwana ta jahar Saidu Mohammed ya ce wadanda suka mutun sun hada da yarinya ‘yar shekara biyu.
Mun samu kiran waya mai daga hankali da safiyar Laraba daga wani mutum Malam Mudassir Abdullahi da misalin karfe 3:57 na safiya, cewa gobara na ci a wani gida.
Nan da nan sai muka tura ma’aikatanmu da kayan aiki don kashe wutar da misalin karfe na asuba,” kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya.
Ya kara da cewa, daga nan sai mutanenmu suka garzaya da wadanda abin ya rutsa da su asibitin kwararru na Murtala Muhammad ana ne likitoci suka tabbatar da rasuwar tasu.
Tuni dai rundunar ta ce ta kaddamar da fara bincike bisa afkuwar al’amarin.