Yadda Gwamna Yahaya Bello ya zafge ma’aitakan sa

Gwamnan jahar Kogi Yahaya Bello yayi zabon zube a Majalisarsa wajen zafge dukkanin ma’aikatan, a ranar Laraba 18 ga Watan Disamba 2019 ne,

Gwamna Bello ya bayyana cewa, matakin hakan zai fara aiki ne nan-take ba tare da wata-wata ba. Gwamnan ya umarci masu rike da mukamai da su mika ragamarsu ga jami’an da su ka fi matsayi a duk ma’aikatar da su ke aiki. Sannan Yahaya Bello  mika godiyar sa ga mutanen da ya zaba su ka yi wa gwamnatin jahar Kogi aiki a matsayin Kwamishinoni.

Sai dai  sallamar da aka yi ba ta shafi sakatariyar gwamnatin jahar ba wato Folashade Ayoade Arike, domin tana rike da mukamin nata kawo yanzu.

Darekta Janar na harkar yada labarai Kingsley Fanwo, ya zama mai bada shawara  kan harkokin yada labarai da sadarwa na gwamnan jahar,kwamishinan kudi Idris Hashiru a da, ya zama mai bada shawara ga gwamna a kan harkokin kasafin kudi da tsare-tsaren na jahar.

The Nation ta rawaito cewa, Momoh Jibril da Yakubu Okala sun dawo kan kujerunsu na babban akawun jahar da kuma babban mai binciken kudi. Mallam Muhammed Onogu ya yi dacen komawa kujerarsa ta babban Sakataren harkokin yada labarai na gwamnatin Yahaya Bello.

Jim kadan da samun nasarar lashe zaben ne gwamna Yahaya Bello ya salami hadiman sa, SA da kuma SSA.

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More