
Yadda gwamnan jahar Bauchi ya auro yar kasar Labnan a matsayin mata ta 2
Gwamnan jahar Bauchi Bala Muhammad wato Kauran Bauchi, ya karbi sabuwar amaryarsa a ranar Asabar 31 ga Agusta 2019, cikin kawayen amaryan da suka kawota sun hada da mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed.
Sabuwar amaryar gwamnan jahar Bauchi, mai suna Natasha Mariana, ta tare a gidan mijinta, Bala Mohammed dake gidan gwamnatin jahar.
A ranar 26 ga Yuli, 2019 Gwamnan jahar Bauchi, Bala Mohammed, ya auro sabuwar amarya balarabiyar kasar Labnan sai dai mazauniyar na gida Najeriya ce,Natasha Mariana itace matar gwamnan ta biyu.
Labarin ya bayyana ne ranar Juma’a inda mai magana da yawun gwamnan Ladan Salihu, ya ce an daura aure ne a masallacin Syriya dake Jahar Legas.
Kauran Bauchi ne gwamnan Najeriya na uku wanda ya kara aure jim kadan bayan darewa karagar mulki.
Ya bi sahun gwamnan jahar Yobe Mai Mala Buni, da kuma gwamnan jahar Nasarawa Abdullahi Sule, wadanda sukayi aure bayan samun nasarar zaben da aka gudanar na 2019.