Yadda gwamnatin Buhari ta zuba triliyan daya a shasen ilimi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta zuba jarin kusan Naira triliyan daya da kwata a sashen ilimin kasar nan tun daga lokacin da ta hau karagar mulki a shekarar 2015. Inda yace an kudaden ne a bangaren ko-ta-kwana da sashen ma’aikata.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da wata cibiyar karatun share fagen digiri na biyu, da Babban Bankin Najeriya, CBN ta gina a Jami’ar ABU da ke  garin Zariya.

Sanarwar da mai bai wa shugaban kasan shawara a kan yada labaru, Femi Adesina ya fitar ga manema labarai, ta yi bayanin cewa shugaban kasan ya kuma bayyana kudirin gwamnatinsa na samar da ingantaccen ilimi ga ‘Yan Najeriya, duk da cewa  ana fuskantar karancin kudin shiga.

Buhari yayi nuni  da cewa za su tabbatar da inganta Jami’ar ta ABU wadda ita ce Firimiyar Arewa, Sardaunan Sakkwato ya kafata da jimawa, ‘‘a rubuce yake a tarihi cewa wannan makarantar ta ba da kyakkyawar gudunmawa ga bunkasa ci gaban kasar nan kuma muna godiya ga wanda ya kafata,” in ji shi. Wakazalika, Buhari ya koka da tabarbarewar kayan aiki a jami’o’in Najeriya, wanda ya ce hakan ya auku ne sakamakon rashin ware musu isassun kudaden ayyuka a shekaru masu yawa da suka gabata.

A karshe shugaba Buhari a yayi kira kan cewa Gwamnati ta dukufa ga samar da kudi ga muhimman makarantun na nan gida Najeriya duba da  da cewa akwai karancin kudin shiga a halin da ake ciki yanzu.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More