Yadda hukumar EFCC ta bankado naira miliyan 65.5 a offishin INEC

Hukumar EFCC ta ce ta bankado fiye da naira miliyan 65.5 a ofishin zaben na jahar Zamfara da ke birnin Gusau.
Hukumar ta sanar cewa ta samu kudaden ne a cikin wasu akwatunan adana kudi masu sulke a ofishin akauta dake kula da kudin hukumar ta INEC.
Kudin dai sun hada da bandir-bandir guda 81 na naira dubu-dubu da bandir 97 na ‘yan dari biyar-biyar da kuma dari biyar-biyar guda 96.

Hukumar EFCC da ke jahar Sokoto ce ta kai samamen ofishin INEC din dake jahar Zamfara, inda tace ta samu korafi ne daga wani ma’aikacin wucin gadi da ya yi aikin zaben 2019 a jahar amma ba a biya shi hakkinsa ba.

Ma’aikacin ya yi zargin cewa ba su samu alawus ba na naira 6000 na aikin zabe da suka yi guda biyu ba, a yadda wasu sukayi korafin cewa ana basu 9000, yayin da Sokoto ke bada 12000.

EFCC ta ce tana zargin kudin na daga cikin kudaden da gwamnati ta saki ga hukumar zabe domin yin aron kujeru da rumfuna ga rumfunan zabe sannan kuma a biya ma’aikata ladan aikin su bayan su gama.
An damko manyan jami’ai hukumar zaben wato INEC ta Zamfara guda 4 tare da jami’an zaben na jahar guda 14.
A binciken da EFCC tayi ta gano cewa shugabannin da suka gudanar da aikin zaben guda 10,500 babu wanda aka biya yadda ya kamata duba da cewa an ware masu naira miliyan tamanin da huda da dubu dari shida da chasa’in da shida. (N84, 696,000)

Duba da cewa anan ana cigaba da bincike sai dai har zuwa yanzu dai hukumar INEC ba tace uffan ba dangane da batun.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More