Yadda jami’an tsaro suka samu miliyan 10 a wajen masu garkuwa da mutane

Jami’an rundunar a jahar Sokoto sun samu zunzurutun kudi wanda yawansu ya kai kimanin miliyan 10 da manyan bindigu kirar AK47 guda 8 a hannun wasu masu garkuwa da mutane da suka sace wani attajirin dan kasuwa Alhaji Tukur Zubairu, a jahar Sokoto.

Da yake gabatar da jawabi ga manema labarai yayin bajakolin masu laifin a hedikwatar rundunar yan sanda masu yaki da aikata fashi da makami (SARS) da ke babban birnin tarayyar Abuja, kakakin rundunar yan sanda ta kasa DCP Frank Mba, ya ce, masu laifin sun hada tawagar aikata ta’addanci a lokacin da suka hadu a gidan yari na Katsina.

Jaridar legithausa ta rawaito cewa,rundunar yan sanda ta kama jimillar masu laifi 81 a sassan Najeriya daban-daban, inda aka samu manyan bindigu kirar AK47 guda 8, carbin alburusai 344, na’ura mai kwakwalwa guda 10 da sauran wasu makamai na gida guda 15, cewar Mba.

Mun hadu a nan ne domin yi muku jawabi a kan kokarin da rundunar yan sanda ke yi wajen tabbatar da tsaro, kamar yadda muka dauki alkawarin gudanar da harkokinmu a bude, ba tare da rufe wani abu ba. Jami’an mu sun yi nasarar kama mambobin wata kungiyar yan ta’adda mai hatsari da wani mai suna Rufai ke jagoranta.Sun hada wannan tawaga ne a gidan yari na Katsina inda aka tsare su sakamakon aikata laifuka daban-daban kafin a yanke musu hukunci.

Babu wanda ya san yadda suka yi suka hada kansu lokacin da suke gidan yari,tun a gidan yarin suka kitsa sace attajirin dan kasuwa na jahar Sokoto Alhaji Tukur Zubairu a cewar Mba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More