Yadda kotu ta tabbatar da nasarar gwamnan Oyo na PDP  

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Kotun sauraren kararrakin zaben gwamna dake zaune a garin Ibadan ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Adebayo Adelabu ya shigar yana mai kalubalantar zaben gwamnan  PDP a Oyo da sunan bai cancanci tsayawa takara ba.

Inda ta tabbatar da Gwamna Seyi Makinde na PDP a matsayin zababben gwamnan  jahar.

Adelabu shi ne tsohon mataimakin gwamnan Bankin Najeriya wato  CBN, yana  kalubalantar zaben gwamna Seyi Makinde wanda aka gudanar a watan Maris 2019.

 Shugaban kwamitin da ke sauraren karar, Sirajo Muhammed ne ya yanke  hukuncin, inda ya tabbatar da cewa mai shigar da karar  Cif Bayo Adelabu na APC ya kasa gabatar da kwararan hujjojin da zasu tabbatar da zarginsa,  wanda hakan ya sabawa dokokin zabe na 2010.

Da yake maida martani, daya daga cikin Lauyoyin da ke bai wa Adelabu kariya, Akin Olujimi, ya ce za su hadu da sauran lauyoyi masu mukamin SAN’s domin nazarin hukuncin kotun.

Inda ya ce daga nan ne za su tabbatar da irin  matakin da ya kamata su dauka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More