Yadda labaran karya ya hada Osinbajo da matarsa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa matarsa Dolapo Osinbajo ta zarge shi  da neman mata bayan da wani hotansa ya bayyana a kafofin sada zumunta tare da wasu mata sanye da tufafi masu nuna tsiraici.

Ya ce, ” mako 3 da suka gabata mamata ta kira ni ta ce, ‘Yemi ashe matan banza ka ke bi yanzu.” ”

Sai dai ya ce abin mamakin shine, a zahiri matan da ya dauki hoto da su a wajen wani taro sanye suke da tufafi na mutunci.

Amma wata kafar yada labarai ta shafin Internet ta yi amfani da hanyoyin sauya hotuna na zamani inda aka sauya kayan matan don a bata masa suna.

Ya ce kafar yada labaran sun buga hoton tare da labarin da ke cewa ‘an kama Osinbajo da matan banza’.

Osinbanjo ya bayyana hakan ne a wani taro da BBC ta shirya don yaki da labaran a duniya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More