Yadda majalisa ta tantance shuwagabannin hukumar NDDC da Buhari ya aika masu

Majalisar dattawa ta tantance wasu mutane uku da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika masu da sunayensu domin ta tantancesu kafin a nadasu mukamin shuwagabannin hukumar kula da cigaban yankin Neja Delta, NDDC. Kamar yadda Jaridar Guardian ta ruwaito

Mutanen uku sune:

  • Pius Odubu
  • Cif Bernard Okumagba
  • Otobong Ndem.

Shugaba Buhari ya nemi majalisar ta amince da nadin Pius a matsayin shugaban hukumar gudanarwar ta  NDDC.

Yayin da ya nemi majalisar ta tantance Bernard domin zama darakta a hukumar da kuma Otobong a matsayin babban darakta mai cikakken iko na kula da sashin gudanar da manyan ayyuka.

A lokacin daya bayyana gaban majalisar, Mista Pius Odubu, tsohon mataimakin gwamnan jahar Edo ya bayyana mata manufarsa na amfani da wannan dama domin kawo karshen tashe tashen hankula da matasa ke janyowa a yankin Neja Delta.

Amma da aka zo kan Bernard Okumagba, sai yan majalisun suka nemi ya ‘rusuna ya tafi’ saboda cancantarsa da kuma kwarewarsa da suka saka shi dacewa da mukami.

An  samu yar hatsayin yayin tantance Otobong. Wani dan majalisa mai suna Sanata Mathew Urhoghide ne ya bayyana cewa bai gamsu da yadda Otobong ya jera bayanan karatunsa a cikin takardar bayanansa na neman aiki ba, daga bisani kuma aka kwantar da hatsaniyar,. kuma majalisar ta amince da shi

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More