Yadda majalisar Amurka ta tsige Donald Trump

Yan majalisar wakilai a Amurka sun jefa kuri’ar da ta tabbatar da tsige Shugaba Donald Trump, bisa wasu laifuka guda biyu.

Shugabar majalisar wakilan Nancy Pelosi ta bayyana cewa ‘yan majalisa 230 sun goyi bayan tsige shugaban yayin da 197 suka ki amincewa.

Laifin Mista Trump na farko shi ne kokarin tursasa shugaban Ukraine da ya binciki abokin hamayyarsa, a zabe mai zuwa, kuma tsohon mataimakin shugaban kasar, Joe Biden.
Laifi na biyu kuwa ya hada da kokarin kawo wa majalisa tarnaki. Mista Trump a yanzu ya zamo shugaba na uku da aka taba tsigewa.

A yanzu dai kallo zai koma ga majalisar dattawa da yan jam’iyyar Republican da shugaban ke da rinjaye domin yi masa shari’ah.
Masana na ganin zai yi wuya su amince da wannan mataki na majalisar wakilai.
BBC ta rawaito cewa, shi kuwa Shugaba Trump ya mayar da martini ne a wani gangami a Michigan, inda yake nuni da cewa ko a jikinsa.

Ya ce na fada a wasikata da na aika wa Pelosi cewa, ci gaba da shirinki na tsigewar da ba ta da amfani, kina saba rantsuwarki ta aiki, kina saba biyayyarki ga tsarin mulki, kin kaddamar da yaki a kan dumokuradiyyar Amurka.
Donald Trump shine shugaban Amurka na uku da aka taba tsige wa a tarihi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More